Iraqi ta haramta alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya
MajaIisar dokokin Iraqi ta zartar da dokar da ta haramta alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya, inda ta yi tanadin hukuncin shekara 10 zuwa 15 a gidan yari ga duk wanda aka kama da karya dokar.
A ƙarƙashin dokar, ƴan daudu za su fuskanci ɗaurin shekara ɗaya zuwa uku.
Masu goyon bayan dokar sun ce zata taimaka wajen bunƙasa biyayya ga tanadin addini a ƙasar.
Amma ƙungiyoyin sa kai sun ce dokar za ta ƙara gogoa wa Iraqi kashin kaji, a tsakanin masu ra'ayin neman jinsi ɗaya.
Masu goyon bayan luwadi da maɗigo da kuma karuwanci, da likitocin da ke yin tiyatar sauya jinsi ga masu buƙata, da kuma ƴan daudu, duk za su fuskanci hukunci a sabuwar dokar.
A baya dai, daftarin dokar da aka zartar a 1980 ta yi tanadin hukuncin kisa ne ga masu neman jinsi.
Sai dai daga baya an yi gyaran fuska ga dokar, bayan fuskantar turjiya daga Amurka da sauran ƙasashen yamma.
Ɗan majalisa, Amir al-Maamouri ya shaidawa kafar Shafaq News, a ranar Lahadi, cewa sabuwar dokar za ta taimaka wajen yaƙi da sabuwar ɗabi'ar neman jinsi da ta bayyana a cikin al'umma, wadda kuma ta saɓawa addinin musulumci da kuma al'adar jama'ar Iraqi.
Ɗan majalisar da ya gabatar da ƙudirin, Raed al-Maliki, ya ce an jinkirta aiwatar da ƙudirin dokar a farkon watan nan ne saboda ziyarar Firaiminista Mohamed Shia al-Sudani Amurka
Ya ce: "Mun yi ƙoƙarin kaucewa ɗaukar matakin da zai shafi ziyarar ne saboda sun ɗauki dokar a matsayin abin da ya shafi ƴan cikin gida kuma basu son a samu shisshigi daga waje".
Masu alaƙar jinsi da ake yi wa laƙabi da LGBT a taƙaice sun daɗe suna fuskantar fushin hukumomi a Iraqi, inda a baya ake afani da dokokin tabbatar da ɗa'a da al'ada wajen hukunta su.
Human Rights Watch da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce sun tattara bayanan garkuwa da mutane da azabtarwa da fyaɗe da kuma kisan kai da dama.
A shekarun baya bayan nan an ga yadda manyan jam'iyyun siyasar ƙasar suke sukar masu neman jinsin, ake kuma ƙona tuttocin su, a wajen zanga zanga da dama.
A cewar ofishin harkokin wajen Amurka dai, aiwatar da wannan doka barazana ne ga ƴancin ɗan Adam da kuma walwala.
Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce Iraqi ta rushe damar da take da ita, ta bunƙasa tattalin arzikin ta, a fannin janyo hankalin masu zuba jari"
Shi ma sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Cameron, ya bayyana dokar a matsayin wani abu mai haɗari kuma na damuwa ga jama'a.