
Shekaru ashirin bayan mamayar Iraqi, har yanzu ana samun ce-ce-ku-ce kan ci gaba da kasancewar makaman ƙare dangi a ƙasar wanda kuma ya nuna da hannun Birtaniya a ciki.
An samu sabbin bayanai a wani bincike da BBC ta yi a kan makaman ƙare dangi bayan shekara 20 da mamayar Iraqi da aka yi musamman ma bayan tattaunawa da gwamman mutane da abin ya shafa.
"Abin mamaki." Wannan shi ne martanin da wani jami’in rundunar M16 ya yi lokacin da wani abokin aikinsa ya faɗa masa a 2001 cewa da gaske Amurka take kan yaƙin Iraqi.
Ga Birtaniya, idan aka zo ɓangaren faɗan abubuwa kan Iraqi, musamman irin barazanar da makaman ƙare dangi na ƙasar ke yi – wani abu ne na yin taka tsan-tsan.
A wani lokaci can baya, an bayyana cewa gwamnatin Birtaniya ta bijiro da zargin mallakar makaman ƙare dangi da ake yi a Iraqi. Sai dai, ministoci a lokacin sun ce an tabbatar musu da cewa babu makaman.
"Yana da muhimmanci a gane cewa irin bayanan sirri da nake samu da su na dogara, kuma ina tunanin cewa da bayanan zan dogara,’’ in ji tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair.
Ya ce a jajiberin ranar da za a ƙaddamar da mamayar, ya yi tambaya – kuma an ba shi tabbaci daga kwamitin haɗaka na tattara bayanan sirri. Ya ƙi yin suka ga kwamitin kan gazawa da ya yi.
Wasu ministoci sun ce suna da shakku a lokacin.
"Kusan lokuta uku, na aza ayar tambaya kan bayanan sirri da Richard Dearlove ya bayar,’’ in ji sakataren harkokin waje, Jack Straw. “na matsu kan bayanan. Sai dai, Dearlove ya tabbatar min cewa za a iya dogara da waɗan nan jami’ai.” Amma, mista Straw ya ce hakan nauyi ne da ya rataya kan ƴan siyasa, saboda sune suke ɗaukar mataki na ƙarshe.
Da aka tambaye shi kan gaza samun bayanan sirri a kan Iraqi, Sir Richard ya ce “A’a. “Har yanzu ina da yaƙinin cewa Iraqi na da wasu makamai sannan an ma tsallaka da wasu kan iyaka zuwa Syria.

Sai dai wasu basu yarda da hakan ba. “babbar gazawa ce,'' in ji Sir David Omand, mai kula da harkokin tsaro da leƙen asiri na Birtaniya a lokacin. Ya ce nuna son kai ya sa ƙwararrun jami'an gwamnati suka saurari bayanan da basu cika ba da ya goyi bayan ra'ayin cewa Saddam Hussein yana da makaman ƙare dangi, tare da rangwame duk wanda ba shi da shi.
Wasu a cikin jami'an MI6 sun ce su ma sun damu. "A lokacin na ji cewa abin da muke yi bai dace ba," in ji wani jami'in da ya yi aiki a Iraki, wanda bai taɓa yin magana ba kuma ya nemi a sakaya sunansa.
"Babu wani sabon labari ko ingantaccen bincike ko sa ido wanda ya nuna cewa Iraqi ta sake fara shirye-shiryen mallakar makaman ƙare dangi da kuma haifar da wata barazana," in ji tsohon jami'in. "Ina tsammanin daga mahangar gwamnati shi ne kawai abin da za su iya samu.
Jami'an MI6 a Iraqi ba su da wani bayani game da makaman ƙare dangi ko kaɗan, kuma akwai buƙatar son sabbin bayanan sirri daga majiyoyi don ƙarfafa batun, musamman lokacin da aka shirya yin takarda a watan Satumba.
Wani jami'i ya tuno yadda ya naɗi wani sakon murya, inda ya ce "babu wata muhimmiyar rawa" ga hukumar leƙen asirin sama da shawo kan al'ummar Birtaniya kan lamarin don ɗaukar mataki. Sun ce an yi tambayoyi idan hakan ya dace, kuma an goge sakon.